Da marecen jiya Talata ne aka kashe wani mai zanga-zanga na yahudawan Heridi da kuma jikkata wasu da dama a birnin Kudus,kamar yadda kafafen watsa labarun Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka ambata.
Tashar talabijin ta channel 12 mai watsa shirinta da harshen Hibru ce ta watsa labarin, tana mai cewa wata motar safa ce ta take masu Zanga-zangar, sai dai kuma tuni ‘yan sanda su ka kama matukin motar.
Wani hoton bidiyo da aka nuna, ya kunshi yadda motar ta safa take cin karo da dandazon yahudawan Heridi masu Zanga-zangar da suke nuna kin amincewa su shiga aikin soja a Isra’ila.
Wanda aka take har ya mutum, saurayi ne dan shekaru 18 kamar yadda kafafen watsa labarun su ka ambata.
Su dai yahudawa Heridi ba su shiga aikin soja a Isra’ila saboda suna daukarta ba kasar da take aiki da addinin yahudanci ba, duk da cewa an yi dokar da ta tilasta musu yin hakan.
Shugabannin wannan kungiyar ta yahudawa suna daukar “Isra’ila” a matsayin kasar da ba ta addini ba, don haka bai kamata a shiga aikin soja a karkashinta ba.
A lokacin yakin Gaza, kwamandojin soja da ‘yan siyasar Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun yi kokarin shawo kan manyan malaman wannan kungiya domin su bari samarinsu su shiga aikin soja, amma sun ki amincewa da hakan, tare da yin barazanar cewa idan aka yi musu tilas za su yi hijira su koma wata kasa ta daban.A ranar 25 ga watan Yuli ne dai aka yi doka a Majalisar Haramtacciyar Kasar Isra’ila wacce ta tilastawa Heridi shiga aikin soja, da kuma hana duk wani taimakon kudi ga makarantunsu na addini, har sai idan sun yi hakan.