Saudiya Ta Yi Maraba Da Tattaunawa Tsakanin Kungiyoyi Masu Gaba Da Juna A Kudancin Yemen

Gwamnatin kasar Saudiya ta yi maraba da bukatar kungiyoyi masu gaba da juna a kudancin Yemen don sasantawa a birnin Rayad babban birnin kasar.  Tashar

Gwamnatin kasar Saudiya ta yi maraba da bukatar kungiyoyi masu gaba da juna a kudancin Yemen don sasantawa a birnin Rayad babban birnin kasar.  Tashar talabijan ta Aljazeera ta kasar Qatar ta nakalto majiyar kasar Saudiya na cewa ta amince da bukatar kungiyoyin na kudancin kasar Yemen na tattaunawa kan matsalolin da suka taso a baya bayan nan don warwaresu.

Wannan na zuwa ne bayan hare-hare ta sama wanda jiragen kawance kasashen larabawa suka kai kanwurare na kungiyar STC wacce take iko da gwamnarin rokin kwarya na kasar ta Yemen, wacce take samun goyon bayan kasar Hadaddiyar daular Larabawa.  STC dai bayan mamayar lardin Hadaral Maut na kasar tana shirin shelanta banlewa daga kasar Yemen, wacce Huthawa daga arewacin kasar suke iko da ita, bayan zaben raba gardama da za’a gudanar nan gaba.  Lardunan Hadral Maut da  Al-Mahra na kasar Yemen suna iyaka da kasar Saudia, kuma bata son STC wacce UAE take goyon baya ta sami iko da larduna saboda zai zama hatsari ga tsaron kasar ta Saudiya.  Gwamnatin kasar ta Saudiya tana goyon bayan wata kungiyar wacce akekara (PLC) tun shekara ta 2014 don yakar Huthawa wadanda suke iko da muhimman wurare a kasar ta Yemen tun lokacin. Kasar Iran ce take goyon bayan gwamnatin Arewacin kasar ta Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted