Duk Da Cewa Yahudawa Basu Fi Kashi 3% Na Yawan Mutanen Amurka Ba Amma Su Suke Jijjuya Gwamnatocin Kasar Saboda HKI

Wani marubu a harkokin diblomasiyya a nan kasar Iran ya bayyana cewa duk tare da cewa ma biya addinin yahudanci a kasar Amurka basu fi

Wani marubu a harkokin diblomasiyya a nan kasar Iran ya bayyana cewa duk tare da cewa ma biya addinin yahudanci a kasar Amurka basu fi kashi 3% ne na yawan mutanen kasar ba amma kuma su suke jujjuya gwamnatocin kasar ta yadda zasu ci gaba da goyon bayana HKI.

Shafin labarai na Parstoday bangaren farisanci ya nakalto Porso Jaafari wani marubu ce a bangaren diblomasiyya a nan kasar Iran yana fadar haka a shafin labarai na ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya kuma kara da cewa.

Wadannan yahudawan sun sami nasarar kaiwa inda suka kai ne bayan hada kan dukkan kungiyoyin yahudawa a kasar a karkashin kema guda wacce ake kira AIPAC .

Ya ce wannan kungiyar ta sami karfi a kasarAmurka har ya kai ga suna da tasiri a dukkan gwamnatozin kasar Amurka da kuma majalisun dokokin kasar, ta yadda babu wata bukatar HKI da zata shiga hannun shuwagabanni yan siysa musamman majalisar dokokin kasar sai sun tabbatar da cewa wannan bukatar ta sami amincewar wadannan yan siyasa.

Manufar AIPAC ita ce tabbatar da tsaro da kuma samuwar HKI a kan kasar Falasdinu da ta mamaye, tare da taimakon manya manyan kasashe duniya.

Kungiyar tana amfani da karfin tattalin arziki da na siyasan da take da shi a kasar Amurka don cimma manufoginta, kuma su suka kai kasar Amurka suka baro a rigingimun da shiga a gabasa ta tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments