Pakistan: An Yankewa Imran Khan Da Matarsa Hukuncin Zama Gidan Kaso Na Shekaru 17

Wata kotu ta musamman a yankin Shahrukh Arjumand a birnin Rawalpindi na kasar Pakisatan ta yanke hukunncin zaman kaso na shekaru 17 kan tsohon fdirai

Wata kotu ta musamman a yankin Shahrukh Arjumand a birnin Rawalpindi na kasar Pakisatan ta yanke hukunncin zaman kaso na shekaru 17 kan tsohon fdirai ministan kasar Imran Khan da kuma matarsa Bushra Bibi, dangane da rigimar Toshakhan na 2. Da kuma wani laifi wanda ya sabawa doka ta 409 na penal Code na kasar Pakistan. Har’ila yau kotun ta ci Imran Khan taran Rs 10 Miliyon.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar kasar ya bayyana cewa wannan hukuncin ya kara dulmuya kasar Pakisatan a cikin rikicin siyasa, ganin yadda Imran Khan yake da magoya baya masu yawa a kasar, wadanda kuma suke ganin an takura masa ne saboda akidarsa ta siyasa a kasar.

Rigimar Toshakhana dai, dangane da kyaututtukan da shuwagabannin suke samu, wanda a doka dole ne a sasu a cikin asusun gwamnati. Amma Imran Khan da matarsa Bushra sun karbi kyauta daga hannun sarakunan kasar Saudiya amma sun kasa maida su  cikin asusun gwamnati.

Tun cikin watan satumban  shekara ta 2024 ne aka fara shari’ar tare da halattar Imran Khan da Matarsa, kuma a gabansu aka yanke masu hukunci tara da kuma zaman gidan kaso.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted