Masu Zanga zanga Sun Yi Cincirindo A Gaban Ginin Majalisar Dokokin Birtaniya

Daruruwan masu zanga zanga ne suka taru a gaban majalsiar dokokin birtaniya a birnin London domin nuna damuwarsu game da ci gaba da kisan kare

Daruruwan masu zanga zanga ne suka taru a gaban majalsiar dokokin birtaniya a birnin London domin nuna damuwarsu game da ci gaba da kisan kare dangin isra’ila a gaza, sun dauki matakin ne domin farkar da duniya kan mawuyancin halin da ake ciki a daidai lokacin da zagayowar haihuwar Annabi Isa ke kara karatowa.

Ci gaba da yayata irin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi wa alummar falasdinu a yankin gaza , ya kara farkar da duniya kan halin da ake ciki, sai dai masu rajin kare hakkin dan adam dake nuna goyon bayansu ga alummar falasdinu na ci gaba da fuskantar tsangwama saboda tsayin Dakar da suka nuna.

Gwamman mutane ne suka taru a westminister domin tunawa da kuma girma dubban falasdinawa da isra’ila ta kashe kusan shekaru 3 ke nan da take kai hare-hare , inda wasu yara suka rera wakokin juyayi domin nuna jimaminsu ga iyalan falasdinawa da suka rasa rayukansu a yankin Gaza, da kuma jan hankali game da takurar da manona falasdinu ke ciki  musamman a lokacin girbin zaytun.

Wadanda suka halarci wajen gangamin sun yi shiru na minti 2 domin tunawa da falasdinawa da lamarin ya shafa, da  kuma wadanda suke ci gaba da gwagwarmayar da suka hada da mutanen 24 da ke gidan yarin isra’ila ,  haka zalika sun ta rera taken kira da a kawo karshen yakin kuma sun yi kira ga gwamnatin birtaniya da ta saurari bukatun wadanda ke yajin aikin ci abinci .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted