Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Matsaloli

Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi da kuma shugaban kasar Azarbaijan Ilham Aleyev a birnin Baku sun tattauna kan dangantakar dake tsakaninsu da kuma

Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi da kuma shugaban kasar Azarbaijan Ilham Aleyev a birnin Baku sun tattauna kan dangantakar dake tsakaninsu da kuma hanyoyin da zaa bi wajen warware kalubalen da ake fuskanta.

Kasashen iran da Azarbaijan suna da alakar aladu da tarihi mai zurfi a tsakaninsu, kuma dukkan bangarorin biyu, sun jaddada game da mihimmancin ci gaba da tattaunawar diplomasiya domin kaucewa rashin fahimta tsakani.

Tattaunawar ta su ta kunshi hadin guiwar siyasa da lamarin da ya shafi makwabta da kuma hanyoyin kyautata dangantaka tsakani , kana kuma ya isar da sakon gaisuwar shugaban kasa mas’ud pezeshkiyan ga shugaban kasar ta Azarbaijan da kuma aniyarsa ta ganin an kara zurfafa danganata tsakaninsu.

Ana san bangaren shugaban kasar Azarbaijan Aliyuv ya bayyana shirinsa na yi amfani da kowwacce irin dama ta kara karfafa dagantaka tsakaninsu,  kuma ya bayyana ziyarar da shugaban iran pezeshkiyan ya kai a baya bayan nan a matsayin mai tarihi, kuma ta taka rawa sosai wajen samar da karin fahimtar juna .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted