Rasha Ta Yi Maraba Da Cire Sunanta A Matsayin ” Barazanar Da Amurka  Teke Fuskanta

Mai Magana da yawun fadar mulkin Rasha Dmitry Viskov ya ce; Fadar mulkin kasar tana maraba da matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka na

Mai Magana da yawun fadar mulkin Rasha Dmitry Viskov ya ce; Fadar mulkin kasar tana maraba da matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka na bitar siyasar tsaron kasar, da ta kunshi cire kasar Rasha a matsayin barazanar da Amurkan take fuskanta.

Viskov ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Tass” cewa; a cikin sabon tsarin tsaron kasar ta Amurka an cire Rasha a matsayin baraza, don haka yana kira da a samo hanyoyin aiki tare akan muhimman batutuwa na duniya.

Haka nan kuma ya ce; Wannan matakin ci gaba ne sosai.

Wannan sabuwar siyasar tsaron ta Amurka tana yi wa China a matsayin babban kalubale ta fuskar tattalin arziki, don hakan Amurka za ta yi aiki domin sake dawo da adalci da kuma abinda ta kira ‘yancin Amurka.”

Sai dai kuma ta jaddada wajabcin ci gaba da jibge sojoji a yankin tekunan Inida da kuma Pacific domin abinda ta ce kokarin hana afkuwar yaki.

Haka nan kuma ya bayyana fatansa na ganin sabuwar siyasar tsaron Amurka ta share fagen kawo karshen yakin kasar Ukirniya da kuma tattaunawa da bude sabuwar alaka da Amurka, da hakan shi ne ra’ayin shugaba Vladmir Putin.

Matakin na Amurka akan Rasha ya bakantawa kasashen turai da suke son Amurkan ta zamar musu jagora a yakin da suke yi da Rasha ta hanyar kasar Ukiraniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted