Sojojin kasashen Afghan da Pakistan sun yi musayar wuta a safiyar yau Asabar, a kan iyakokin kasashen biyu.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan budewa juna wuta ya nuna cewa yarjeniyar tsagaita budewa juna wuta na kasar saudiya a kwanakin baya ya kasa aiki.
Hukumomin kasashen biyu sun tabbatar da cewa sojojin kasashen nasu sun yi musayar wuta a daren Jumma’a wayewar garin asabar. Tare da amfani da makamai masu linzami . Ko wani bangare yana zargin dayan da fara bude wuta.
Zabihullahi Mujahid kakakin gwamnatin kasar Afganistan ya rubuta a shafinsa na X kan cewa, sojojin kasar Pakisatan ne suka fara bude wuta a kan iyakar kasar da ke Spin Boldak a cikin lardin Kandahar a daren Jumma’a sannan sojojinsa kasar suka maida martani.
A bangaren kasar Pakisatan kuma kakakin Firai ministan kasar Shahbez Sharif ya bayyana cewa sojojin Afganisatan ne suka fara budewa sojojin Pakisatan wuta a kan iyakar kasashen biyu da ke Chaman.