Afirka ta Kudu Za Ta Dauki Hutu Daga Halartar Tarukan G20 A Karkashin Shugabancin Trump

A ranar Alhamis ne fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta sanar da cewa kasar za ta dauki hutu daga halartar tarukan G20 yayin da

A ranar Alhamis ne fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta sanar da cewa kasar za ta dauki hutu daga halartar tarukan G20 yayin da shugaban Amurka Donald Trump ke jagorantar kungiyar a karkashin tsarin karba-karba, bayan da gwamnatinsa ta tabbatar da cewa ba za ta gayyaci Afirka ta Kudu a taro mai zuwa ba.

Amurka ta karbi shugabancin G20  na karba-karba a makon da ya gabata, bayan kauracewa taron da Shugaba Cyril Ramaphosa ya shirya a Johannesburg.

“A wannan lokacin a shekara mai zuwa, Birtaniya za ta karbi shugabancin G20. Za mu iya shiga cikin batutuwan da suka shafi duniya,” in ji mai magana da yawun Ramaphosa, Vincent Magwenya.

“A yanzu haka, za mu dakatar da shirye-shiryen kasuwanci har sai lokacin da muka sake dawowa a cikin dukkanin harkokin kungiyar,” in ji shi a wani rubutu da ya yi a shafukan sada zumunta.

Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya tabbatar a ranar Laraba cewa “Afirka ta Kudu ba za ta iya shiga cikin duk wani taron G20 a shekara mai zuwa ba,” yana mai cewa “Shugaba Trump da Amurka ba za su mika goron gayyata ga gwamnatin Afirka ta Kudu don shiga cikin tarukan G20 a lokacin shugabancinmu ba.” Inji shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted