Dakarun Gwagwarmaya A Kasar Iraki Sun Kai Hari Kan Cibiyar Samar Da Wutar Lantarki Ta Isra’ila

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun gwagwarmaya a kasar Iraqi sun kaddamar da wani sabon hari kan Isra’ila inda suka samu wata cibiyar samar da wutar

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun gwagwarmaya a kasar Iraqi sun kaddamar da wani sabon hari kan Isra’ila inda suka samu wata cibiyar samar da wutar lantarki a birnin Telaviv a ci gaba da mayar da martani da suka yin a hare-hare da kisan gillan da HKI ke yi wa Falasdinawa,

A wata sanarwa da gamayyar dakarun yaki da ta’addanci a kasar iraki suka fitar a safiayr yau Alhamis suna nuna cewa sun yi amfani da jirgi mara matuki na Kamikaze wajen tarwatsa wata cibiyar samar da wutar lantarki na Isra’ila dake birnin Telaviv , ko a jiya ma sai daisuka kai hari kan filin saukar jiragen sama na Ben Gurion har sai sau biyu

Haka zalika kungiyar ta nuna cewa za ta ci gaba da kai hari kan Isra’ila har sai ta dakatar da kisan kare dangi da take yi a Gaza, da ta fara tun daga ranar 7 gaatan Oktoba da ya gabata wanda yayi sanadiyar mutuwar falasdinawa 32000 mafi yawanci mata ne da yara kanana sama da 74000 kuma suka jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments