Iruwani: Tuhume-tuhumen Da Ake Yi Wa Iran Akan Yemen Ba Su Da Tushe

Jakadan jamhuriyar Musulunci ta Iran a MDD ya yi watsi da tuhume-tuhumen da Amurka da Birtaniya suke yi wa Iran akan abubuwan da suke faruwa

Jakadan jamhuriyar Musulunci ta Iran a MDD ya yi watsi da tuhume-tuhumen da Amurka da Birtaniya suke yi wa Iran akan abubuwan da suke faruwa a tekun “Red Sea’ da Yemen.

Amir Sa’id Iruwani ya  rubuta wasika zuwa shugaban kwamitin tsaro na MDD a jiya Litinin da a ciki ya kore dukkanin zarge-zargen da a ka yi wa Iran a yayin zaman kwamitin tsaro na ranar 14/ Maris/2024.

Iruwani ya kuma ce; Abin takaici ne cewa wakilan Amurka da Birtaniya sun yi amfani da wannan zaman inda su ka dora wa Iran alhakin abinda yake faruwa a tekun “Red Sea’alhali babu tushe a cikin abubuwan da su ka ambata.

Wakilin na Iran a kwamitin tsaron ya kuma ce; Iran ba ta lamunta da wadannan zarge-zargen ba tun daga tushensu, kuma Washington da London suna son yin amfani da hakan ne domin shimfida siyasarsu, da kuma halarta wa kansu hare-haren da suke kai wa Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments