Kasar  Congo Ta Dawo Da Hukuncin Kisa A Kasar Bayan Dagewa Na Kimani Shekaru 20

Gwamnatin kasar Congo Democradiyya ta bada sanarwan cewa ta dawo da hukuncin kasa a kasar,saboda ganin yadda masu aikata laifi a gabacin kasar suna tsira

Gwamnatin kasar Congo Democradiyya ta bada sanarwan cewa ta dawo da hukuncin kasa a kasar,saboda ganin yadda masu aikata laifi a gabacin kasar suna tsira da laifuffukan da suka aikata ba tare da an yi masu hukuncin da ya dace ba.

Shafin labarai na yanar gizo Afirca News ya bayyana cewa gabacin kasar Congo tana fama da rigingimu da tashe tahen hankula na lokaci mai tsawo, kuma a halin yanzu yankin yana da kungiyoyin dauke da makamai kimani 120 inda kungiyar yan tawaye ta M23 take mamaye da yankuna masu yawa a gabacin kasar.

Kungiyar M23 dai wacce ake zargin cewa kasar Rwandace take goya mata baya, tana iko da yankunan gabacin kasar ta Congo kuma ta kori miliyoyin mutane a wasu yankunan yankin zuwa birnin Goma babban birnin yankin.

Ma’aikatar sharia ta kasar Congo ta bada sanarwa a ranar Jumman da ta gabata kan cewa an dawo da hukuncin kisa a kasar, kuma za’a yi amfani da hukuncin kan wadanda suka aikata manya manyan laifuffuka wadanda suka hada da cin amanar kasa, fashi da makami, data zaune tsaye ko kuma aikin banga a kasar.

Kasar Congo dai ta yi watsi da irin wannan hukuncin ne a shekara ta 2003, amma Jean-Claude Katende shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil’adama ya bayyana cewa dawo da wannan hukuncin ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar. Kuma baya ganin dawo da wannan hukuncin zai dawo da zaman lafiya a yankin Kivu mai cike da rikici a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments