Tanzania: MDD Ta Yi Kira Da A Yi Bincike Akan Daruruwan Mutanen Da Aka Kashe Sanadiyyar Rikcin Zabe

A jiya Talata ne dai MDD ta yi kira da a gudanar da bincke akan kashe-kashen da aka yi sanadiyyar zaben da aka yi a

A jiya Talata ne dai MDD ta yi kira da a gudanar da bincke akan kashe-kashen da aka yi sanadiyyar zaben da aka yi a watan karshe.

Wannan kiran na MDD ta zo ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar ta Tanzania su ka tuhumi wasu daruruwan mutane da cin amanar kasa saboda Zanga-zangar  kin amincewa da zabe da su ka yi.

Shugaban hukumar kare  hakkin bil’adama a karkashin MDD Volker Turk ya ce; Da akwai Alamar cewa gwamnatin kasar ta Tanzania tana kokarin batar da dalilai abinda ya faru.

Da akwai rahotanni da suke nuni da cewa jami’an tsaro suna kokarin dauke gawawwakin wadanda aka kashe daga dakunan ajiyar gawawwaki na asibitoci domin batar da su.

Turk ya kira yi jami’an gwamnatin kasar ta Tanzania da su mika gawawwakin wadanda aka kashe a sanadiyyar rikicin zaben ga iyalansu domin binnewa.

Turk ya ce; Da akwai rahotanni da suke nuni da cewa iyalan wadanda aka kashe suna yawo ko’ina,a tsakanin ofisohin ‘yan sanda da asibitoci domin gano gawawwakin dangi da ‘ya’yansu.

Jam’iyyar adawa ta Chadema ta ce adadin wadanda aka kashe din sun kai 2,000 a cikin kwanaki  uku da su ka biyo bayan zabe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted