Qalibaf: Iran Da Pakistan Zasu Aiwatar Dukkan Yarjejeniyar Da Suka Cimma A Tsakaninsu

Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran ya jaddada muhimmancin aiwatar da kuma kammala yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin Iran da Pakistan Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad

Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran ya jaddada muhimmancin aiwatar da kuma kammala yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin Iran da Pakistan

Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqir Qalibaf, ya jaddada muhimmancin matakin da ake dauka a yanzu na dangantakar da ke tsakanin Iran da Pakistan a dukkan fannoni na hadin gwiwa. Ya bayyana ziyararsa zuwa Pakistan a matsayin wani bangare na kokarin da ake yi na fadada dangantaka, musamman hadin gwiwar yankin tsakanin kasashen biyu.

A cikin wata sanarwa da ya aike wa kamfanin dillacin labaran Iran ‘IRNA’ bayan ya isa birnin Islamabad, fadar mulkin kasar Pakistan, a safiyar Laraba, Qalibaf ya ce: “Iran da Pakistan, a matsayin kasashe makwabta, suna jin dadin hulda daban-daban a fannin tattalin arziki, siyasa, da kuma harkokin majalisa, musamman idan aka yi la’akari da yanayin da ake ciki a dangantakar kasashen biyu da kuma yanayin yankin.”

Ya kara da cewa: “Kasashen biyu suna mai da hankali kan hadin gwiwar kasuwanci, siyasa, da tsaro, tare da hadin gwiwa mai inganci tsakanin hukumomin gwamnati a Tehran da Islamabad.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted