Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya

Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a wata hira da yayi da gidan talabijin din Aljazeera ya gargadi isra’ila kuma yayi cikakkan bayani kan

Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a wata hira da yayi da gidan talabijin din Aljazeera ya gargadi isra’ila kuma yayi cikakkan bayani kan shirin nukiliyar iran na zaman lafiya , da kuma halin da yankin ke ciki da yi yuwar sake komawa teburin  tattaunawa da kasar Amurka.

Wannan bayani yazo ne adaidai lokacin da lamura ke kara zafi a yankin  bayan yakin da aka yi tsakanin iran da kuma Israila,  don haka bayanan na Araqchi wata sanarwa ce dake nuna shirin iran na mayar da martani amma kuma tabar kofar tattaunawar diplomasiya  a bude.

Har ila yau ministan ya bayyana cewa iran a shirye take ta tunkari duk wani kalu-bale, kuma za ta mayar da martani mai karfi game da duk wani wuce gona da irin Isra’ila, don mun shirye fiye da kowanne lokaci a baya, kuma yayi gargadin cewa isra’ila za ta sake shan wani kayen idan ta kara shelanta yaki akan iran a nan gaba,

Yace isra’ila tana kokarin kara fadada rikicin yanki ne ta hanyar kai hari kan abubuwan manfetur din kasar iran, yace isra’ila ba za ta iya shiga wani yaki ba ba tare da samu amincewar Amurka ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted