Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da cewa daga lokacin da aka tsayar da wuta zuwa yanzu adadin Falasdinawan da HKI ta kashe sun

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da cewa daga lokacin da aka tsayar da wuta zuwa yanzu adadin Falasdinawan da HKI ta kashe sun kai 200, yayin da wasu  kusan 600 sun jikkata.

Sanarwar ta ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta kuma ci gaba da cewa; A cikin sa’o’i 48 da su ka gabata,an sami shahidai 22, biyar daga cikinsu basu dade da yin shahada ba, sai kuma 17 da aka tono su daga karkashin baraguzai. Haka nan kuma na kai wasu 9 zuwa asibitocin da suke a yankin.

Wani sashe na sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ya ce, har yanzu da akwai shahidai masu yawa da suke a karkashin baraguzai, wasu kuma a kan hanyoyi, saboda rashin kayan aiki da kungiyoyin agaji za su yi amfani da su.

Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu, adadin shahidai ya kai 68,858, sai kuma wani adadin da ya kai 170,664 da su ka jikkata.

Amma daga tsayar da wuta a ranar 11 ga watan Oktoba zuwa yanzu, an sami shahidai da sun kai 226, sai kuma wasu 594 da su ka jikkata. Haka nan kuma an iya tsamo gawawwakin shahidai daga cikin baraguzai har su 499.

Haka nan kuma ma’aikatar kiwon lafiyar tra sanar da karbar gawawwaki 30 da HKI ta mika wa bangaren Falasdinawa ta hannun hukumar agaji ta “Red-Corss.

Tun bayan tsagaita wutar yaki, har ya zuwa yanzu dai HKI tana ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted