Marubucin nan na Najeriya wanda ya sami kyautar Nobel ta Adabi, Wole Soyinka ya bayyana cewa kasar Amurka ta janye izinin shiga Amurka na “Visa” da ta ba shi a shekarar da ta gabata.
Marubucin dan kasar Najeriya dan shekaru 91 ya furta cewa a shekarar 2016 ya keta ‘koren kati” da Amurka ta ba shi, tare da yin watsi da hakkinsa na zama a Amurka, saboda nuna kin amincewarsa da zabar Donald Trump a matsayin shugaban kasa a zangonsa na farko.
Soyinka ya kuma ce an bukace shi da ya sake jaddada neman izinin shiga cikin kasar ta Amurka,sai dai bai bayyana cewa ko zai sake neman visa din ba.
A ranar Talatar makon da ya shude ne dai Soyinka ya nuna wa ‘yan jarida wata wasika da karamin ofishin jakadancin Amurka dake birnin Ikko ya aike masa, da aciki yake nemansa da ya kai passort dinsa domin soke visa da aka ba shi.
Marubucin dan Najeriya ya kuma ce; A halin yanzu ba shi da visa ta zuwa Amurka, don haka wadanda suke gayyatar shi, sun san inda yake a Najeriya idan suna son ganinshi.
A shekarar 1986 ne dai aka bai wa Soyinka kyautar Nobel na adabi, kuma yana zuwa Amurka ne domin koyarwa a jami’o’in Ive League dake gabashin kasar.