Yemen : An yi jana’izar babban hafsan sojin kasar Shahid al-Ghamari a Sana’a

A Yemen Dubban daruruwan mutane ne suka fito titunan birnin Sana’a domin jana’izar babban hafsan hafsan sojin kasar, Laftanar Janar Mohammad Abd al-Karim al-Ghamari, wanda

A Yemen Dubban daruruwan mutane ne suka fito titunan birnin Sana’a domin jana’izar babban hafsan hafsan sojin kasar, Laftanar Janar Mohammad Abd al-Karim al-Ghamari, wanda aka ayyana shahadarsa a hare-haren da Isra’ila ta kai a watan Agusta…

Taron dai ya nuna matukar hadin kan al’ummar kasar, da suka fito daga sassan babban birnin kasar da larduna daban-daban, tare da manyan jami’an soji da wakilan gwamnati.

Jama’a na dauke da hotunan marigayi Janar din, tutocin kasar Yemen, da tutoci masu nuna goyon baya ga gwagwarmayar Falasdinu da kuma yin Allah wadai da harin Amurka da Isra’ila.

Tashar Al Mayadeen ta bayar da rahoton cewa, dubun dubatar ‘yan kasar ne suka halarci jana’izar, yana mai nuni da irin yadda jama’a ke girmama shahid al-Ghamari. A cikin wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin a ranar Alhamis din da ta gabata, Rundunar Sojin Yaman ta sanar da cewa Janar al-Ghamari ya yi shahada yayin da yake gudanar da ayyukansa na goyon bayan Falasdinu. Sanarwar ta kuma jinjina mishi da abokansa a matsayin “mujahidai masu tsayin daka” wadanda suke da himma da gogewa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted