M D D Ta yi Kira Da A Kawo Karshen Yakin Gaza Da Aka Kwashe Shekaru 2 Ana Yi.

Adaidai lokacin da ake taron cika shekaru 2 da fara yakin Gaza Babban sakatare janar din Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya sake yin kira

Adaidai lokacin da ake taron cika shekaru 2 da fara yakin Gaza Babban sakatare janar din Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya sake yin kira da a gaggauta cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta din din din a yankin Gaza .inda ya bayyana yakin a matsayin babban bala’I da ba’a taba ganin irinsa ba

Yakin ya jawo mummunar asarar rayukan mutane fararen hula da kuma lalata abubuwan amfani na jama’a , kuma ya jawo matsaloli masu yawa a ayyukan jin kai da yake bukatar kulawa ta gaggawa da kuma warware matsala ta hanyar siyasa

Guterres ya halarci wannan taron ne inda yayi alkawarin ganin an kawo karshen yakin Gaza kuma ya amince da dukkan shawarwarin da Amurka ta bayar na kawo karshen yakin da tabbatar da zaman lafiya.

Kwanaki kadan bayan da hamas ta kai harin 7 ga watan oktoba a Isra’ila , jagoran juyin musulunci na kasar Iran Ayatollah imam khamina’I ya bayyana cewa kayen da gwamnatin sahyuniya ta sha ba zaa taba mantawa da shi ba, a bangaren soji da kuma leken Asiri, yayin da dama suka yi Magana kan galabar da aka samu kan Isra’ila, kana ya jadda cewa wannan rashi ne da ba zaa iya gyarashi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted