Iran: Dakarun Ruwa Na Iran A Shirye Suke Su Shiga Yaki Da Kowa Don Kare Kasa

Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdurrahim Musawi yay aba da shirin sojojin ruwan kasar na fuskantar duk wani harin da makiya zasu kawowa

Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdurrahim Musawi yay aba da shirin sojojin ruwan kasar na fuskantar duk wani harin da makiya zasu kawowa kasar daga yanzun,

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Musawi yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda ya kai ziyarar aiki a sansanin sojojin ruwa na sojojin kasar da kuma na rundunar IRGC a lardin Hurmuzgan.

Musawi ya ganewa idanunsa makamai na kariya da kuma na kai hare-hare kan makiya wadanda rundunonin ruwa a bangarorin biyu suke da shi da kuma lafiyar sojojin, inda ya bayyana amincewar sa da shirye-shiryen nasu.

Musawi ya kara da cewa daga karshen kallafeffen yakin kwanaki 12 wanda HKI da kuma Amurka suka dorawa kasar a cikin watan yunin da ya gabata. An gabatar da sauye sauye da kuma shirye-shirye masu muhimmanci a cikin sojojin ruwa na kasar, wanda ya kara karfin sojojin.

Musavi har’ila yau ya ziyarci banganen dakarun IRGC na ruwa, inda ya ganewa idanunsa irin tanajin da suke ciki don fuskantar duk wata barazana daga makiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted