Shugaban Iran:Wadanda Suka Fice Daga Yarjejeniyar JCPOA Ke Da Alhakin Halin Da Ake Ciki.

Rahotanni sn bayyana cewa shugaban kasar Iran Masud pezeshkyan  ya gana da shugaban  kungiyAr tarayyar turai Antonio costa a gefen taron majalisar dinkin duniya a

Rahotanni sn bayyana cewa shugaban kasar Iran Masud pezeshkyan  ya gana da shugaban  kungiyAr tarayyar turai Antonio costa a gefen taron majalisar dinkin duniya a birnin newyork,Kuma ya fadi cewa wadanda suka fice a tattaunawar JCPOA su suka haddasa aka fada a halin da ake ciki yanzu.

Har ila yau ya kara da cewa Iran  bata da niyyar mallakar makamin nukiliya kuma ba za ta taba nemansa  ba, don haka Tehran a shirye take ta yi hadaka domin fayyace gaskiya da kuma karyata zarge-zarge marasa tushe balle madafa da ake yi mata kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya.

Yace nauyi ya rataya ne a wuyan wanda suka fice daga yarjejeniyar JCPOA , wato shugaban Amurka ke nan da ya fice daga cikin yarjejeniyar a shekara ta 2018 da aka cimma tsakanin iran da kungiyar tarayyar Turai kan shirin iran na nukiliya da ake takaddama akai .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted