Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar.

Rahotanni sun bayyana cewa an fara taron ministocin harkokin wajen kasashen larabawa da na musulmi a birnin Doha na kasar Qatar, domin share fage na

Rahotanni sun bayyana cewa an fara taron ministocin harkokin wajen kasashen larabawa da na musulmi a birnin Doha na kasar Qatar, domin share fage na taron shuwagabannin kasashen da zaa yi gobe litinin in mai duka ya kaimu , domin tattaunawa kan harin baya bayan nan da Isra’ila ta kai Qatar,

Taron zai tantance matakin diplomasiya da zaa dauka kan hari da Isra’ila takai kasar  Qatar a yankunan fararen hula da zimmar kasashe jamai’an kungiyar Hamas, harin yayi sanadiyar shahadar mutane 5 har da jami’an tsaron kasar  Qatar, kuma harin ya fuskancin yin tir daga kasashen duniya.

Taron gaggawar da kungiyar kasashen musulmi  oic ta kira yana nuna yadda ake goyon bayan kasar Qatar a yankin, da kuma nuna damuwarsu kan laifukan da HKI ke tafkawa a gaza da sauran yankunan da ta mamaye,  kuma ana saran shuwagabannin kasashen za su tattauna kan taswirar hanyar da kasashen larabawa da na musulmi za su bi kan batun, da kuma matsin lambar diplomasiya  ta hanyar majalisar dinkin duniya.

Kimanin wakilai daga kasashen 50 ne za su halarci taron da suka hada da Iran, Turkiya, Pakistan, da kuma Indunusiya .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted