Dubban magoya bayan kungiyar Hizbullah ta kasar labanon ne suka gudanar da gagarumar zanga-zanar a cikin dare a birnin berut domin nuna adawa game da shirin Amurka da HKI na neman yan majalisar dokokin kasar su amince da batun kwance dammarar kungiyar hizbullah.
Bukatar , wanda manzon musamman na Amurka tom barak ya mika, da yan majalisar suka amince da shi wanda ministocin yan shi’a suka yi watsi da shi, sun bakaci ya kasance sojojin gwamnati ne kawai za su rike makamai, wanda ke ishara ga hakkin hizbullah na mallakar makamai don kare kanta, lamarin da yan gwagwarmaya da magoya bayansu suke ganinsa a matsayin wani mataki ne na kai tsaye na Amurka da isra’ila don matsin lamba da zai jefa kasar cikin mawuyacin hali,
Ana ta bangaren kungiyar hizbullah ta yi watsi da wannan shirin baki daya, kuma ta bayyana hakan a matsayin take hakkin dan labanon na kare kansa daga cin zalin Isra’ila, kuma an zartar da shi ne karkashin matsin lamba daga kasashen waje ba tare da cimma matsaya ta kasa ba.