Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa 79 A Yankin Zirin Gaza

Falasdinawa 79 ne suka yi shahidai sakamakon tashin gobara da farmakin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai zirin Gaza a jiya Laraba Majiyoyin kiwon lafiya

Falasdinawa 79 ne suka yi shahidai sakamakon tashin gobara da farmakin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai zirin Gaza a jiya Laraba

Majiyoyin kiwon lafiya sun sanar a cikin dare cewa: An kashe Falasdinawa 79 sakamakon tashin gobara da hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata, ciki har da mutane 16 da ke jiran agaji.

Majiyar ta bayyana cewa, an mayar da shahidai 25 zuwa Asibitin Al-Shifa, 6 zuwa asibitin Sheikh Radwan, 7 zuwa Asibitin Al-Ahli Arab Baptist, 5 zuwa Asibitin Rehabilitation Hamad, 1 Asibitin Al-Awda, 12 zuwa Asibitin Shahidai Al-Aqsa, 23 kuma zuwa Asibitin Nasser.

Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun ci gaba da kai farmaki a zirin Gaza, inda suka kai farmaki a gabashin Hasumiyar Hamad dake arewacin Khan Yunus, inda suka yi ruwan bama-bamai a tantunan ‘yan gudun hijira da suka rasa matsugunansu da ke kusa da hasumiyar Italiya da ke unguwar Al-Nasr a birnin Gaza, tare da jefa bama-bamai a kan gidan iyalan Habib da ke unguwar Al-Sabra da ke birnin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkata wasu da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted