Baqa’i Ya Ce: Iran Zata Kare Muradunta A Zaman tattaunawanta Da Tawagar Kasashen Turai

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da kasar China, da kuma batun makamashin nukiliya na kasar Iran. Baqa’i ya bayyana cewa: Yarjejeniyar shekaru 25 tsakanin Iran da China ta fara aiki kuma tana ci gaba. Ya kuma kara da cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana da kyau kuma tana ci gaba, yana mai jaddada cewa: Iran na daukar muhimmanci sosai kan dangantakarta da China, kuma ziyarar shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian za ta kasance wani muhimmin sauyi wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma karfafa matsayin Iran a cikin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai “SCO”.

Baqa’i ya bayyana cewa, kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai tana wakiltar “tsari mai inganci na hadin gwiwa tsakanin kudu da kudu,” yana mai cewa, wannan kungiya, tare da kungiyar BRICS, na iya ba da damammaki masu yawa ga kasashe masu tasowa don bunkasa shirye-shiryensu na raya kasa. Ya yi la’akari da cewa kungiyar a yanzu ta ƙunshi fiye da kashi 40% na al’ummar duniya da kusan 20% na GDP na duniya, wanda ya sa ta zama “mai tasiri a cikin dangantakar kasa da kasa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted