Sudan: Dakarun RFS Sun Kashe Fararen Hula 24 A El-Fasher

An kashe mutane 24 tare da raunata wasu 55 a harin da Dakarun  Kai Daukin Gaggawa suka kai kan birnin El Fasher Kungiyar likitocin kasar

An kashe mutane 24 tare da raunata wasu 55 a harin da Dakarun  Kai Daukin Gaggawa suka kai kan birnin El Fasher

Kungiyar likitocin kasar Sudan ta sanar a jiya Alhamis cewa: Fararen hula 24 ne suka mutu sannan wasu 55 da suka hada da mata 5 suka samu raunuka sakamakon luguden wuta da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kai ranar Laraba a garin El Fasher dake arewacin Darfur.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarto cewa, an kai harin ne a tsakiyar kasuwa da unguwar Awlad al-Reef, inda ya bayyana lamarin a matsayin wani kisan gilla da aka yi da gangan kan fararen hula da ba su dauke da makamai.

A cikin sanarwar da ta fitar, cibiyar ta yi Allah wadai da kakkausar murya da abin da ta bayyana a matsayin “mummunan laifuffuka,” tare da jaddada cewa hakan na kara kaimi ga jerin laifuffukan yaki da kisan kiyashi da aka shafe sama da shekara guda ana yi wa mazauna garin El Fasher, a cikin wani killace da ke fama da matsalar karancin abinci, magunguna da kayayyakin more rayuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted