Ministocin harkokin waje na Iran da Saudiya sun bukaci hadin kan kasashen musulmi don magance matsalolin da al-ummar falasdinu take faskanta a gaza. Sun bayyana cewa akwai bukatar kasashen musulmi su san yadda zasu yi don nisar da abinci zuwa yankingaza da kuma kawo karshen kissan kiyashin da HKI take yi a yankin.
Tashar taabijin ta Presstv ta bayyana cewa Abbas Aragchi ya tattauna da tokwaransa na kasar Saudia Faisal bin Farhan al-Saud ne a gefen taron ministocin harkokin waje na kasashen musulmi OIC na gaggawa wanda aka gudanar a birnin Jidda na kasar Saudiya .
Banda haka ministocin sun yi maganar karfafa dangantaka tsakanin kasashen wadanda suka hada da kasuwanci, yawon shakatawa, da kuma al-adu. Sun kuma ya magana dangane harkokin tsaro a yankinn Asiya ta yamma, da kuma hanyoyin kawo karshen matsalolin da suke faruwa a cikinsa.