Iran Da Rasha; Tawagar Turai Ba Su Da Hurumin Dawo Da Takunkumi Kan Iran

Ministocin harkokin wajen kasashen Iran da Rasha sun bayyana cewa: Tawagar Turai ba ta da ikon yin amfani da kudurin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya

Ministocin harkokin wajen kasashen Iran da Rasha sun bayyana cewa: Tawagar Turai ba ta da ikon yin amfani da kudurin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya kan Iran

Ministocin harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Rasha sun bayyana cewa: Tawagar kungiyar tarayyar Turai ba ta da hurumin shari’a da kyawawan dabi’u wajen yin amfani da hanyar da za ta bi wajen dawo da kudurorin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da aka soke.

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi da takwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov sun yi musayar ra’ayi a cikin wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho kan abubuwan da suka shafi batun Shirin makamashin nukiliyar kasar Iran, musamman matakin da kasashen Turai uku wato Birtaniya da Jamus da Faransa suka dauka a jajiberen cikar wa’adin doka mai lamba 2231 na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da kuma batun hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa.

A cikin wannan tattaunawa, an jaddada cewa: Kasashen uku na Turai, saboda gazawarsu wajen sauke nauyin da suka rataya a wuyansu a karkashin shirin hadin gwiwa na (JCPOA) a daya bangaren, da kuma goyon bayan da suke baiwa Amurka wajen kai wa Iran hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliyarta na zaman lafiya, a daya bangaren, sun aikata wani babban laifi ga kuduri mai lamba 2231, don haka ba su da hurumin doka da dabi’u na dawo da kudurin da kwamitin tsaro na JCPO ya yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted