Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Gargadin Bullar Rikici A Sudan Ta Kudu Da Zai Shafi Kasashen Yankin

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin barkewar rikici a Sudan ta Kudu da kuma barazanar da yake yi ga kasashen makwabta Majalisar Dinkin Duniya ta

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin barkewar rikici a Sudan ta Kudu da kuma barazanar da yake yi ga kasashen makwabta

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa sabon fadan dauke da makamai a Sudan ta Kudu tsakanin dakarun da ke biyayya ga shugaban kasar Salva Kiir Mayardit da mataimakinsa na farko Riek Machar na iya kara ruruta wutar rikici da kuma yaduwa zuwa kasashen da ke makwabtaka da ita, a daidai lokacin da al’amuran jin kai ke kara tabarbarewa a kasar.

Mataimakiyar Sakatare-Janar ta Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin Afirka Martha Pobe ta bayyana a yayin zaman kwamitin sulhu na ranar 18 ga watan Agusta cewa “aikewa da sojojin da ake yi a halin yanzu da kuma ayyukan da ake ci gaba da yi na iya haifar da karuwar tashe-tashen hankula tare da kara rura wutar rikici tsakanin al’ummomin yankin.”

Ta kara da cewa ci gaba da wannan yanayin “zai iya canza yanayin rikici da kuma haifar da shiga tsakani daga kasashe makwabta.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted