Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Wani Mummunan Hari Kan Gaza

Sojojin mamayar Isra’ila sun kai wani mummunan farmakin kan birnin Gaza tare da janyo ruftawar gidaje a Khan Yunis Falasdinawa da dama sun yi shahada

Sojojin mamayar Isra’ila sun kai wani mummunan farmakin kan birnin Gaza tare da janyo ruftawar gidaje a Khan Yunis

Falasdinawa da dama sun yi shahada tare da jikkata a yau Juma’a a wani kazamin harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Gaza a rana ta hudu a jere, yayin da gwamnatin mamayar Isra’ila take ci gaba da mamaye birnin. A halin da ake ciki kuma an ci gaba da rusa gidaje a Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza.

Majiyar Asibitin Al-Shifa ta sanar da cewa: Falasdinawa biyu sun yi shahada yayin da wasu suka jikkata a harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai unguwar Al-Rimal da ke yammacin birnin Gaza.

Wakilin gidan talabijin na Aljazeera ya bayar da rahoton cewa: Sojojin mamayar sun gudanar da aikin rusa gine-gine guda biyar cikin mintuna 15 a safiyar yau a unguwar Al-Zeitoun da ke birnin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted