Jakadan Iran a kasar Rasha ya bayyana cewa: Sharuɗɗan sake tattaunawa da Amurka ba su cika ba
Kazem Jalali, jakadan Iran a kasar Rasha ya bayyana cewa: A halin yanzu, bisa ga hujjojin da ake da su, ba a cika sharuddan sake tattaunawa da Amurka ba na kai tsaye ba, domin har yanzu Amurkawa ba su yi yunkurin gyara halayensu ba, ko kuma akalla sun bayyana matsaya kan wannan batu.
A wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Rasha RIA Novosti a jiya Juma’a, yayin da yake amsa tambaya kan sharuddan da Iran ta gindaya na ci gaba da gudanar da wani sabon zagayen tattaunawa a kaikaice da Amurka, biyo bayan hare-haren da sojojin gwamnatin Amurka da yahudawan sahayoniyya suka yi kan Iran, Jalali ya kara da cewa: A yanzu haka al’ummar Iran na ci gaba da gabatar da muhimman tambayoyi game da tattaunawar.
Ya ce, “Idan har aka shirya gudanar da tattaunawar ba tare da wasu sharudda da suka dace ba, kuma idan aka yi amfani da wadannan shawarwarin a matsayin shirin yaudara, wace amana za a ba wa daya bangaren?”
Jalali ya kara da cewa hare-haren da Amurka da yahudawan sahayoniyya suka yi wa Iran ya tabbatar da cewa an rusa dokokin kasa da kasa a fagen duniya, kuma ka’idojin da aka bi da su doka ce ta daji.