Babban Sakataren Kungiyar Hizbullahi Ya Ce; A Shirye Suke Su KaluBalantar Makiya Babu Batun Mika Kai

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya jaddada cewa; A shirye suke su kalubalanci makiya, babu batun mika kai daga gare su Babban sakataren

Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya jaddada cewa; A shirye suke su kalubalanci makiya, babu batun mika kai daga gare su

Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Qasem ya bayyana a wajen taron tunawa da babban jagoran jihadi Hajj Ali Karaki (Abu al-Fadl Karaki) cewa: Shugaban da ya yi shahada yana daya daga cikin mataimaka a majalisar jihadi ta Sakatare Janar kuma fitaccen mutum ne da ya cancanci a san aikinsa da rawar da ya taka.

Babban sakataren ya kara da cewa: Shahidi Ali Karaki ya taka rawa wajen tsara harin neman shahadan Ahmed Qasir, tare da hadin gwiwar shugaban shahidai Hajj Imad Mughniyeh.

Sheikh Qassem ya jaddada cewa: Gwagwarmaya ta kasance tushen kwanciyar hankali ga kasar Labanon, tare da hana makiya yahudawan sahayoniyya aiwatar da duk wani wuce gona da iri na tsawon shekaru 17 da kuma dakile ayyukan ginin matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a kudancin Lebanon, tare da maye gurbin mamayar da ‘yantar da su.

Ya kara da cewa, a cikin shekaru 42 da suka gabata, gwagwarmaya ta samu nasarori masu inganci, musamman ‘yantar da kasar Labanon da kuma hana gwamnatin mamayar Isra’ila cimma burinta a lokacin harin ta’addancin watan Yulin shekara ta 2006.

Ya yi nuni da cewa, gwagwarmayar da aka yi a yakin “Oli al-Bas” ya dakile yunkurin makiya na isa birnin Beirut, tare da hana sojoji da jami’an nanayar Isra’ila 75,000 shiga kan iyakar kasar da ke kudancin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted