Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa iran zata bude sabuwar kofar tattaunawa da Amurka ne kawai idan a shirye take da yi adalci babu takurawa daga kasashen yamma.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, kasashen yamma da Amurka da kuma kasashen yamma suna barazanar kara takurawa kasar Iran idan har take komawa kan teburinn tattaunawa kan shirinta na makamashin nukliya.
Haka ma kasashen Turai guda uku E3 Faransa Jamus da Burtaniya sun bukaci Iran ta koma kan teburin tattaunawa kan shirinta na makamashin Nukliya. Ko kuma su sake takura mata da takunkuman tattalinn arziki. Amma Tehran ta bayyana cewa ba zata shiga tattaunawa a cikin halin da aka sab aba, dole ne sai ta sami lamuni kan cewa za’a yi mata adalci a kuma bata hakkinta na tshe makamashin Uranium kamar yadda yarjeniyar NPT ta tanadar.
Aragchi ya bayyana haka a taron jakadun kasashen waje a nan Tehran, musamman E3 da kuma EU gaba daya.
Abbas Aragchi ya bayyana cewa ya tattauna kan tsaye ta Vidio Confrens da ministocin harkokin wajen E3 inda ya fada masu cewa Amurka ce ta fice daga JCPOA a shekara ta 2018 ba Iran ba sannan itace ta bar teburin tattaunawa ta zabi yaki a cikin watan Yunin da ya gabata. Don haka Iran ba zata sake shiga tattaunawan da za’a ci gaba da cutar da ita ba. Ta zabi dakatar da tattaunawa duk tare da barazanar sake farfado da takunkuman tattalin arziki a kanta..