Shahid HajiZade babban kwamandan sojojin Iran a bangaren kera makamai masu linzami shahid Hajizade kafin shahadarsa ya bayyana cewa, jagoran juyin juya HKI, tun da dadewa ya ce musu su maida hankali kan tabbatar da cewa makamansu masu linzaminsu suna fadawa dai-dai inda ake son su fada.
Tashar talabijin ta Presstv wacce ta sanya hoton bidoyin shahid Hajizade ya na cewa: gas hi a halin yanzu, godiya ta tabbata ga All..mun cimma wannan manufar. Kuma makamai masu linzami na kasar, musamman wadanda aka yi amfani da su a wa’adussadik na daya da na biyu sun tabbatar da aikin namu.
Major General Amir-Ali Hajizadeh dai shi ne babban kwamandan sojojin IRGC mai kula da makamai masu linzami da dukkan abubuwan da suka shafi sararin samani.