Shugaban Amurka Donald Trump ya bai wa Rasha wa’adin kwanaki 50 na kawo karshen ayyukan soji a Ukraine, inda ya yi barazanar sanya takunkumin tattalin arziki mai tsanani da suka hada da harajin kashi 100 cikin 100 kan kayayyakin da Rasha ke shigowa da su kasarsa, idan har ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba har zuwa wa’adin.
A wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da sabon Sakatare Janar na NATO Mark Rutte, Trump ya sanar da wani gagarumin shiri na wadata kasar Ukraine da dimbin makaman Amurka, da suka hada da na’urorin tsaron makami mai linzami na Patriot, ta NATO, a matsayin wani bangare na yarjejeniyar da ta shafi kasashen NATO, karkashin jagorancin Jamus.
Jaridar Washington Post, ta nakalto daga wasu majiyoyi inda ta watsa rahoton cewa: An kiyasta sabon kunshin taimakon sojojin Amurka ga Ukraine ya kai kimanin dala biliyan 10, kuma mai yiwuwa ya hada da izinin yin amfani da sabbin makaman kai hare-hare, ciki har da makamai masu linzami 18 na ATACMS masu cin dogon zango da ake jibge a Ukraine.