Burtaniya, Faransa Da Jamus Sun Kaskantar Da Kansu A Lokacinda Suka Goyi Bayan Hare-Haren HKI Kan Iran

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin sharia da kuma kasa da kasa ya ce kasashe uku na turai Burtaniya da Faransa da kuma

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin sharia da kuma kasa da kasa ya ce kasashe uku na turai Burtaniya da Faransa da kuma Jamus sun kada mutuncinsu a lokacinda suka giye bayan yakin kwanaki 12 wadanda HKI da Amurka suka dorawa JMI.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazen Gharibabadi yana fadar haka a hirar da yayi a wata tashar talabijan a nan Tehran a jiya Lahadi.

Jami’in diblomasiyyan ya kara da cewa wadannan kasashe uku sun gabatar da hujja marasa karfi a goyon bayan da suka bawa HKI da Amurka hujjar kaiwa Iran hare-hare. Kuma sune hujjojin da Amurkan da kuma HKI suka bayar a kwamitin tsaro na farwa kasar da yaki.

Kafin su fara yakin HKI da Amurka sun mika takardu wadanda a cikinsu suka shaidawa kwamatin tsaro na MDD kan cewa zasu fadawa Iran da yaki ne saboda hanata mallakar makaman Nukliya.

Yace: Gwamnatin kasar Iran tana da yencin maida martani a kan wadannan kasashe guda biyu. Banda wadannan kasashe uku, babuwata kasar turai da ta goyi bayan HKI a yakin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted