NYT: Natanyahu Yana Tsawaita Yaki A Gaza Don Ci Gaba Da Kasancewa Kan Iko A HKI

Jaridar NYT ta kasar Amurka ta bayyana cewa firai ministan HKI Benyamin Natanyaho da gangan yake tsawita yaki a Gaza don tsawaita zamansa a kan

Jaridar NYT ta kasar Amurka ta bayyana cewa firai ministan HKI Benyamin Natanyaho da gangan yake tsawita yaki a Gaza don tsawaita zamansa a kan kujerar shugabancin kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani binciken da Jaridar New York Times ta yi, inda take cewa Natanyahu ya san cewa matukar ya sauya matsayinsa na shugaban gwamnatin HKI to kuwa sammashin kamasi da kuma tuhume-tuhumen da ake masa zasu tashi wadanda zasu zama masa matsala, kuma a lokacin hatta gwamnatin Amurka ba zata iya yi masa wani taimako ba.

An fara yaki a Gaza ne a ranar 07 ga watan octoban shekara ta 2023 . daga lokacin ya zuwa yanzu sojojin Natanyahu sun kashe falasdinawa kimani 57,000. Sannan an jikata wasu fiye da 12000. Banda haka sun rusa fiye da kasha 90% na gaza. Sannan sun hana shiga abinci da ruwa har ya kaiga falasdinawa da dama sun mmutan saboda yuwan da rashin lafiya da wasu dalilai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted