Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Lardin Hodeidah Na Kasar Yemen

Sojojin gwamnatin yahudawan sahayoniyya sun kai hare-hare kan  tashar jiragen ruwa na Hodeidah a kasar Yemen Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan

Sojojin gwamnatin yahudawan sahayoniyya sun kai hare-hare kan  tashar jiragen ruwa na Hodeidah a kasar Yemen

Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan tashar ruwan Hodeidah da ke yammacin kasar Yemen, biyo bayan barazanar da sojojin kasar suka yi a yammacin jiya Lahadi.

Majiyar Yemen ta fada a yammacin jiya Lahadi cewa: An ji karar fashewar abubuwa masu yawa a tashar jiragen ruwa na Hodeida, sakamakon farmakin da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a yankin.

A cewar majiyoyin cikin gidan Yemen, sama da fashe fashe 20 ne aka samu a Hodeidah sakamakon hare-haren da jiragen saman yakin Isra’ila suka kai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted