Kamfanin dillancin Labaran Assosciated Press ta bayyana cewa ana ci gaba da sukar Amurka da HKI kan cibiyoyin kisa da suka kafa a Gaza da sunan tallafawa Falasdinawa da abinci.
Labarin ya bayyana cewa ya zuwa yanzu Amurka da HKI sun kashe Falasdinawa kimani 635 wajen karban abinda suka kira taimakon abinci bayan sun sa su yunwa mai tsanani wanda zai sa su dole su fito su ne mi aminda zasu a sa a cikinsu. Amma idan sun so sojojin HKI su kashesu.
Kamfanin dillancin labaran Associeated Press ya nakalto kamfanoni Amurka guda biyu wadanda sun ce sun shigar da kara Amurka da kuma HKI kan yadda suke gudanar da cibiyoyin rabon abinda suka kira abinci a gaza, wanda bai dace ba.
Kamfanin sun bayyana cewa jami’an tsaron da Amurka da HKI suka kawo a cibiyoyin, da alamun an basu izinin su kashe falasdinawa da suka fito karban abinda suka kira a gaji. Su kuma yi amfani da yuwan da suka sa su don tilasta ,masu fita da kuma kashe su daga karshe.
Wani kamfanin rabon abincin agajin ya ce sojojin na barin wuta kan Falasdinawa hatta kan wadansa suke layin karban agajin.