Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Matsayin Kasarsa Na Rashin Mika Wuya Ga ‘Yan Kama Karya

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta san mika wuya ba, kuma tana rubuta tarihin mutunci da jinin shahidanta A jawabin da

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta san mika wuya ba, kuma tana rubuta tarihin mutunci da jinin shahidanta

A jawabin da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi bayan halartar jana’izar shahidan Quds ya jaddada cewa: Iran ba ta san ma’anar mika wuya ba, yana mai fayyace cewa tarihi zai shaida cewa Iraniyawa sun zubar da jininsu tare da kin ba da kasarsu da mutuncinsu.

Araqchi ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa: “Duk da zafi da rashi na shahidansu kwatsam, amma tunaninsu yana nan a cikin zukatan masu hankali, da kuma zukatan al’ummomi masu zuwa, kuma suna sane da yin riko da Imani da hanyarsu, kuma za su ci gaba da bin tafarkinsu.”

Ya kara da cewa: Za a iya ruguza cibiyoyi da gine-gine da kuma ababen more rayuwa duk muhimmancinsu, amma za su dawo da karfi da daukaka tare da shudewar zamani, sai dai girman al’umma yana da daraja kuma ba ya misaltuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted