Shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa HKI zata yi nadamar hare harenb da ta kai kan wasu wurare a nan kasar Iran wanda ya kai ga shahadar wasu manya manyan jami’an tsaro da kuma msana fasahar Nukliya na kasat.
Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya ce shugaban ya bayyana haka ne a safiyar yau ya kuma bayyana cewa za’a gudanar da taro na majalisar ministocin kasar don tattauna wannan batun.
Labarin wanda shugaban ya aika a shafinsa na internet ya bayyana cewa nan gaba kadan shugaban zai yi jawabi ga mutanen kasar Iran don jin abinda aka shirya don fuskantar ayyukan ta’adanci da HKI ta fara kan kasar a safiyar yau,