Kungiyar ta’addanci ta Da’ish ko ISIS ta zargi shugaban gwamantin kasar Siriya al-Julani da yin sujjada a kofar shiga wajen kafirai
Kungiyar ta’addanci ta Da’ish ko ISIS ta bayyana shugaban sabuwar gwamnatin Siriya Abu Muhammad al-Julani a matsayin azzalumi wanda ya sayar da addininsa tare da yin sujjada a kofar shiga wajen kafirai. Ta yi kira ga ‘yan kasashen waje da ke cikin jami’an tsaron Siriya da su tuba su yi watsi da hidimar da suke yi wa azzalumi.
A cikin wani sako na addini, a kokarinta na jan hankali masu saurarenta wadanda ta kira su “masu hijira saboda Allah,” kungiyar ta’addanci ta ISIS ta fitar da wani kira na farfaganda ga wasu ‘yan kasashen waje da kuma sabbin hukumomin tsaro na gwamnatin Siriya, kungiyar ISIS ta yi kira ga ‘yan kasashen waje da ke kasar Siriya da su tuba su daina yi wa sabon shugaban gwamnatin Siriya Abu Muhammad al-Julani biyayya da hidima, wanda ta bayyana shi a matsayin azzalumin da ya sayar da addininsa tare da yin sujada a kofar mashigar kafirai.
Sakon kungiyar ta ISIS na kunshe da gargadi mai tsanani ga wadanda ke ci gaba da aiki a cikin sabuwar gwamnatin Siriya. Har ila yau, sakon ya hada da barazanar kai hare-haren soji, da nuna kasancewar mambobinta da ta tura su zuwa yankunan karkara, tare da yin barazanar mayar da martani ga duk wani mataki da aka dauka kanta.