A cikin wani wanda Kungiyar Tarayyar Turai ta fitar, ta bayyana cewa ta kirayi jakadanta da ke Jamhuriyar Nijar sakamakon caccakar da hukumomin kasar suka yi wa kungiyar kan gudanar da wasu ayyuka na agaji ba tare da hadin gwiwa da hukumomin kasar ba.
Hakan dai yana zuwa ne bayan da Nijar ta caccaki jakadan Tarayyar Turan tare da zarginsa da raba kimanin euro miliyan 1.3 ga kungiyoyi masu zaman kansu a kasar ba tare da sanar da hukumomin kasar ba, wanda kuma hakan ya sabawa dukkanin dokoki na kasa da kasa.
Tarayyar Turai ta yanke shawawar kiran jakadanta da ke Yamai ne domin tattaunawa da shi kan batun.
Mahukuntan na Jamhuriyar Nijar dai sun bukaci Karin bayani kan yadda aka sarrafa wadannan kudade da kuma bangarorin da aka bawa su. Da kuma kuma ayyukan da ake nufin aiwatarwa da kudaden.
Tun lokacin da sojoji suka karbi ragamar mulki a jumhuriyar Nijar dai ana samun batutuwa da ake kai ruwa rana a kansu, a tsakanin mahukuntan na Jamhuriyar Nijar da kuma wasu daga cikin kasashen yamma musamman kasar Faransa a kan wasu batutuwa da suka shafi ayyukansu a cikin jamhuriyar ta Nijar.