Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jajantawa kan harin ta’addanci da aka kai a arewa maso yammacin Pakistan.
A cikin wasikar ta’aziyya a ranar Alhamis, Pezeshkian ya bayyana juyayi ga gwamnati da al’ummar Pakistan, da ma iyalan wadanda harin ya rutsa da su.
Akalla mutane 42 ne suka mutu tare da jikkata wasu da dama a lokacin da wasu gungun ‘yan ta’addar takfiriyya suka bude wuta kan wasu motocin fasinja dauke da fararen hula mabiya mazhabar Shi’a a yankin arewa maso yammacin Pakistan mai fama da rikici.
Jami’an yankin na Pakistan sun ce harin ya faru ne a ranar Alhamis a Kurram, wani yanki mai tsaunuka na ban mamaki a lardin Khyber Pakhtunkhwa, mai makwabtaka da Afghanistan.
Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka kai a yankin a shekarun baya-bayan nan kan mabiya Shi’a na Pakistan.
A halin yanzu jami’an tsaron Pakistan na ci gaba da gudanar da ayyukan leken asiri a yankuna daban-daban na kasar.