A cikin bayanai daban-daban da ta fitar gwamnatin Amurka ta yi watsi da hukuncin kotun hukunta manyan laifuka na bayar da sammacin kamo Netanyahu da ministan yakin Haramtacciyar kasar Isra’ila kan aikta laifukan yaki a Gaza.
Joe Biden ya bayyana matakin Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya na neman kama Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa a matsayin “abin takaici”.
“Sammacin da ICC ta bayar na kama shugabannin Isra’ila abin takaici ne,” in ji Biden a wata sanarwa da ya fitar.
“Bari na sake bayyanawa ƙarara cewa: duk abin da ICC za ta nuna, ba za a haɗa Isra’ila da Hamas ba.
Y ace Za mu kare Isra’ila daga duk wata barazana ga tsaronta daga kowa.”
Kafin wannan lokacin da kwanaki biyu Amurka ta yi watsi da wani daftarin kudiria kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya da ke yin kira da a dakatar da bude wuta a Gaza.