‘Yan sanda a Pakistan sun ce akalla mutane 25 ne suka rasa rayunkansu sannan wasu fiye da 40 suka jikkata a wani harin bam da aka kai a wata tashar jirgin kasa mai cunkoson jama’a a lardin Balochistan.
Fashewar ta faru ne a daidai lokacin da fasinjoji kusan 100 ke jiran jirgin kasan da misalin karfe 8:45 na safe (03:45 agogon GMT) a Quetta, babban birnin Balochistan.
Babban Sufeton ‘yan sandan yankin Muhammad Baloch ya ce sojoji 14 na daga cikin wadanda suka mutu, da ma’aikatan jirgin kasa guda shida.
Tuni kungiyar’ dake ikirarin samar da Yancin Balochistan (BLA) ta dauki alhakin harin.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce wani dan kunar bakin wake ya auna sojojin da ke tashar jirgin kasa.
Lardi mafi girma kuma mafi talauci a Pakistan, dake raba iyaka da Afghanistan da Iran, yanki ne mai arzikin albarkatun kasa, saidai kuma ya kasance yanki na ‘yan tada kayar baya dake kai hare-hare akai-akai.