Hukumar kare hakkin bil’adam ta MDD ta yi gargadi akan yadda sojojin HKI suke cigaba da kashe mata da kananan yara a zirin Gaza.
Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu adadinFalasdinawan da HKI ta kashe sun haura 43,000 wadanda kuma ta jikkata kuma sun haura 102,000,mafi yawancisu mata da kananan yara.
Hukumar kare hakkin bil’adam ta MDD ta bayyana cewa kaso 70% na wadanda yakin Gaza ya ci,mata ne da kananan yara.
Bugu dakari, yakin na Gaza ya jefa kaso 85% na mutanen yankin cikin matsalolin rashin abinci da magani saboda yadda HKI ta hana shigar da su.
Wani jami’in kungiyar farar hula ta kasar Norway ya bayyana abinda ‘yan sahayoniya suke yi a Gaza da cewa laifin yaki ne.