An sami hatsaniya a wajen filin wasan kwallon kafa a birnin Amsterdam na kasar Holland sanadiyyar fada a tsakanin magoya bayan kungiyar wasan Maccaby Tel Aviv da ‘yan kasar Holland saboda sauke tutar Falasdinu daga saman wani gida a cikin birnin da kuma yaga ta.
Masu goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Maccaby Tel Aviv ne su ka saukar da tutar ta Falasdinu daga saman wani gida, lamarin da ya fusata mutanen Holland da ya sa su ka far musu da duka.
An baza ‘yan sanda a cikin birnin na Amsterdam domin dawo da tsaro.
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa an jikkata 10 daga cikin masu goyon bayan kungiyar kwallon kafar tasu, wasu biyu kuma sun bace.
Da dama daga cikin masu fafutuka da rajin kare Falasdinawa a kasar ta Holland sun fusata lokacin da su ka fahimci cewa da akwai kungiyar kwallon kafa ta Isra’ila a cikin kasar tasu.
Kwanaki kadan da su ka gabata kafafen watsa labarun HKI sun ce, kungiyar leken asiri ta Mosad ce za ta yi wa ‘yan wasan rakiya zuwa Holland domin yin wasa da Ajacson Amsterdam.