Mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Harris da tsohon shugaban kasar Donald Trump suna hankoron ganin sun samu nasara a jihohi 7 masu muhimmanci a zaben shugaban kasa.
A muhimman jihohin da ke kan gaba a fafatawar ta 2024, ana iya cewa babu wata tazara sosai tsakanin abokan hamayyar biyu a zaben Amurka da za a gudanar kasa da sa’o’i 24.
A ƙarkashin ƙundin Tsarin Mulkin Amurka, manyan shugabannin baya da suka kafa ƙasar sun tabbatar da cewa kowace jiha daga cikin guda 50 da ake da su, suna da ‘yancin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.
A tsarin zaben Amurka , kowace jiha tana da adadin ƙuri’un “wakilain masu zabe,” bisa ga yawan al’ummarta. Yawancin jihohi suna da tsarin karba-karba wanda ke bai wa duk wanda ya lashe zaɓen fidda gwani damar samun kuri’u.
Kowane dan takara na bukatar kuri’u 270 daga cikin 538 don samun nasara, akwai yiwuwar samun sakamakon zaɓen daga cikin ƴan tsirarun jihohin da ake kira “swings state”, wadanda suke da tarihin lashe zabe tsakanin ‘yan takarar jam’iyyar Republican da Democrat.