Kasar Iran Ta Gama Shirya Tsarin Mayar Da Martaninta Kan Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Ba zai yiwu a iya bayyana cikakkun tsarin martani “Alkawarin Gaskiya” na 3 ba

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Ba zai yiwu a iya bayyana cikakkun tsarin martani “Alkawarin Gaskiya” na 3 ba

Mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran Birgediya Janar Ali Fadavi, a yayin da yake mayar da martani kan wata tambaya game da ranar da za a fara aiwatar da harin “Alkawarin Gaskiya na 3” a matsayin martani ga harin da ‘yan sahayoniyya suka kai wa Iran, ya jaddada cewa ba za a iya bayyana cikakken shirin ba, amma tabbas za a aiwatar da shi.

Birgediya Fadavi ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar yayin bikin ranar yaki da girman kai da aka gudanar a jami’ar fasaha ta Sharif a ranar Litinin 4 ga watan Nuwamba, inda ya ce, wasu kasashen larabawa suna samar da kayayyaki ga ayyukan yahudawan sahayoniyya, kuma wannan na daya daga cikin abubuwan al’ajabi a duniya.

Da yake mayar da martani ga wata tambaya game da ranar da za a fara aiwatar da mayar da martani na “Alkawarin Gaskiya na 3”, ya jaddada cewa ba za a iya bayyana hakikanin ranar ba, amma babu shakka za a aiwatar da shi.

Birgediya Janar Fadwi ya yi nuni da cewa: Daya daga cikin sifofin yakin Gaza shi ne fallasa karyar da aka shafe shekaru 96 ana yi kan ‘yan sahayoniyya, yana mai cewa: Mutane a duniya sun fahimci cewa an yi musu karya tsawon shekaru 96, kuma sun gano cewa yahudawan sahayoniyya wasu ‘yan mamaya ne, sannan sun gano gaskiya da aka boye shekaru da yawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments